<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><title>Cikin Yesu Almasihu Zan Dogara LW183</title>
<lyrics>[V1]
 1) Cikin Yesu Almasihu zan dogara.
 Aikin ceto duk ya cika, zan dogara,
 Ba a cikin aiki nawa,
 Ko a cikin nagartata,
 Sai dai cikin aikin Yesu zan dogara.

[V2]
 2) Cikin giciyen Almasihu, ga gafara.
 Ko mutane ba sa yarda, ga gafara.
 Fansarmu wurinsa ta ke,
 Almasihu Mai Cetonmu,
 Giciyen ya kai mu gunsa, ga gafara.

[V3]
 3) Jinin Ubangiji Yesu ya wanke ni.
 Jininsa mai daraja ne, ya wanke ni.
 Laifina mai dauɗa baki,
 Jininsa ya tsarkake ni.
 Cikin jininka, ya Yesu, ka wanke ni.

[V4]
 4) Cikin ƙaunar Almasihu, ga hutawa.
 Ta fi ƙaunar iyayenmu, ga hutawa.
 Ƙaunarsa fa ba kamarta.
 Ko zunubi, ko jaraba,
 Yesu ne zai ci nasara, ga hutawa.

[V5]
 5) Zuwan Yesu Almasihu na gaskata.
 Bisa ga alkawarinsa, shi ne zai dawo.
 Zo da sauri, Ubangiji,
 Sake halina da jiki,
 Taka ce sarautar kome har abada.</lyrics>
<hymn_number>183</hymn_number>
</song>